Tarihin sabon Sarkin Zazzau Ahmad Nuhu Bamalli – BBC News Hausa

0
7

Bayan jan ƙafa ta tsawon mako biyu da gwamnatin jihar Kaduna ta yi wajen naɗa sabon Sarkin Zazzau sakamakon mutuwar Sarki Shehu Idris, a ƙarshe Gwamna Nasiru el-rufa’i ya sanar da naɗa Ahmed Nuhu Bamalli.

Bari mu yi nazari kan waye wannan sabon sarki da Masarautar Zazzau ta samu wanda shi ne na 19 a jerin sarakunan masarautar.

Ahmad Nuhu Bamalli ya fito ne daga gidan Mallawa, kuma shi ne Magajin Garin Zazzau kafin naɗinsa sarki a ranar Laraba.

Ambasada Ahmed ɗa ne ga Nuhu Bamalli tsohon Magajin Garin Zazzau kuma tsohon minista a Najeriya.

Magajin garin Zazzau wanda masani shari’a ne da diflomasiyya shi ne jakadan Najeriya a Thailand a yanzu.

Saboda girman sarautarsa ta Magajin Garin Zazzau da kuma kusancinsa da gwamnati shi ya sa aka dinga sanya shi a jerin waɗanda ka iya zama sabon Sarkin Zazzau na 19.

Mahaifinsa, Nuhu Bamalli, yana cikin mutanen da suka yi fafutukar samun ‘yancin kan Najeriya kuma ya taba zama ministan harkokin wajen kasar sannan ya rike sarautar Magajin Garin Zazzau, wadda Alhaji Ahmed ya gada bayan rasuwarsa a 2001.

Sabon sarkin na Zazzau ya yi karatun firamare da sakandare a garin Kaduna, sannan ya tafi Jami’ar Ahmadu Bello, Zaria inda ya yi Digirinsa na farko a fannin lauya a 1989.

Kazalika ya yi Digirin Master’s a fannin harkokin kasashen duniya da diflomasiyya a Jami’ar ta Ahmadu Bello a 2002.

Jami’o’in da ya halarta domin yin wasu kwasa-kwasai sun haɗa da Harvard da Oxford da Northwestern University da ke Chicago da kuma Jami’ar Pennsylvania da ke Amurka.

Ahmed Nuhu Bamalli ya yi kusan ɗaukacin rayuwarsa ta aiki ne yana aiki a bankuna inda ya taɓa yin aiki a kamfanin da ke buga kudɗn Najeriya, Nigerian Security Printing and Minting.

A shekarar 2017 ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya naɗa shi a matsayin jakadan kasar a Thailand.

Sabon sarkin na Zazzau yana da mata ɗa, Mairo A Bamalli da kuma ‘ya’ya biyar – namiji ɗaya da mata huɗu.

© 2020 BBC. BBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba. Karanta hanyoyin da muke bi dangane da adireshin waje.

Source: https://www.bbc.com/hausa/labarai-54438563

Ahmed Nuhu Bamalli,Emir of Zazzau

Actu monde – NG – Tarihin sabon Sarkin Zazzau Ahmad Nuhu Bamalli – BBC News Hausa

Abonnez-vous à notre chaîne Youtube en cliquant ici

Vidéo du jour: De la cocaïne retrouvée dans une école maternelle de Seine Saint Denis, deux enfants hospitalisés